Thursday, 1 June 2017
Dalilin Da Ya Sa Hukumar JAMB Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 76,925

Home Dalilin Da Ya Sa Hukumar JAMB Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 76,925
Ku Tura A Social Media


Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire a Nijeriya wato JAMB ta ce ta ki fitar da sakamakon dalibai 76,925 saboda zargin da take masu da yin magudi a yayin jarrabawa.
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyade shi ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Laraba a babban birnin tarayya Abuja.

Farfesan ya ce su na kan bincike akan lamarin, kuma da zaran sun kammala, za su fitar da sakamakon wadanda ke da gaskiya.

Ya kara da cewa, izuwa yanzu sun saki sakamakon mutane 1,606,901 a cikin 1,718,425 da suka zana jarrabawar.

“Sauran sakamako guda 80,889 kenan” inji farfesan “muna sane muka rike 76,925 saboda zargin magudi”

Ya ce sauran za su fito nan ba da dadewa ba
Daure ka/ki yi sharhi:

Share this


Author: verified_user

0 Comments: