Uncategorized

An Sayar Da Dabinon Da Kasar Saudiyya Ta Aiko Nijeriya A Matsayin Sadaka

An Sayar Da Dabinon Da Kasar Saudiyya Ta Aiko Nijeriya A Matsayin Sadaka

Wani lamari mai ban takaici ya auku a kasar nan, inda wasu suka sayar da dabinon da kasar Saudiyya ta aiko da shi sadaka ga al’ummar Nijeriya domin a raba wa mabukata masu azumi.

A kwanakin baya ne hukumomin Saudiyya suka aiko da dabino tan dari biyu, domin a raba wa mabukata a iajeriya, inda maimakon a raba sadaka, sai wasu suka karkatar da shi suka sayar.

Mai magana da yawun ma’aikatar al’amuran kasashen waje, Clement Aduku ya tabbatar da cewa dabinon ya iso ma’aikatarsu, amma an raba shi ga hukumomin da suke da alhakin rabawa. Ya ce ba da miyan ma’aikatarsu bane wasu suka karkatar da dabinon zuwa na sayarwa. Don haka ya ce za a gudanar da bincike domin gano, wadanda ke da hannu cikin badakalar domin hukunta su.

©Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button