Kannywood

Zaben MOPPAN: Maikano ya doke Lere, Ciroma


A ranar Lahadi ne aka rantsar da sabon Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Kasa, MOPPAN, bayan an gudanar da zabe a Kano.

Sabon Shugaban, Abdullahi Maikano, ya kada abokan takarar sa biyu, Yakubu Lere da Al’amin Ciroma. Dukkan ‘yan takarar su uku daga Kaduna suke, kasancewa a wannan zaben an kayyade cewa daga bangaren Kaduna shugaban kungiyar zai fito.

Tashin farko dai takara ta yi zafi kusan fiye da sauran zabukan kungiyar da aka taba yi a baya, saboda wasu dalilai. Kowane dan takara ya tashin haikan ya na yakin neman zabe, a Kaduna, Kano da sauran jihohin Arewa.

Zaben da aka kada kuri’a da asubahi, bayan an kashe dare ana tantance ‘yan takara da masu zabe, ya zo da bazata, ganin yadda Maikano ya yi wa sauran ‘yan takara rata mai nisan gaske.

Yayin da ya zo na daya da kuri’a 57, Lere ne ya zo na biyu da kuri’u 54, shi kuma na uku, wato Al-amin Ciroma ya samu kuri’u 13. Zaben dai wakilai 5 daga kowace na Arewacin kasar nan masu ruwa da tsaki a harkar fim suka jefar kuri’un, a zaben da aka gudanar cikin zauren taron Otal din Royal Tropicana, Kano.

MOPPAN, wacce a Turance ke nufin Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria, kungiya ce mai kunshe da sauran kungiyoyin ‘yan fim tun daga na wasa, furodusoshi, editocin finafinai, daractoci da sauran su.

Alhaji Abdulkarim Mohammed, shugaban kamfanin shirya finafinai na Moving Image ne shugaban kungiyar na farko, daga shi sai Alhaji Sani Mu’azu sai kuma Dakta Umar Faruq Jibrin, mai kamfanin Kwality, malamin jam’a a BUK, kuma tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Kano, wanda shi ya sauka, bayan an kafa kwamitin riko ne daga baya aka shirya zabe.

Wannan zabe na MOPPAN ya dau zafi ta hanyoyi da bangarori da dama. Na farko dai a tsakanin su kan su ‘yan takara, a baya an sha samun takun-saka da ‘yar tsama a tsakanin Lere da Maikano, dukkan su manyan furodusoshi a Kaduna. Dama kuma Maikano ya dade ya na harin shugabancin kungiyar, bai samu ba, sai a wannan karo.

Wata matsala wacce ita ce ake zargin alamomi ko dalilan zargin tsoma bakin gwamnatin Jihar Kaduna a cikin sha’anin zaben, ita ce batun Lere, wanda a zahiri ya yaki takarar Nasiru El-Rufai a 2015, bakin rai bakin fama, a matsayin sa na shugaban gidan radiyo mallakar gwamnatin jihar Kaduna, a zamanin mulkin Ramalan Yero.

Idan za a iya tunawa, Lere ne jami’in gwamnati na farko da aka fara sallama daga cikin gyauron gwamnatin Ramalan Yero, kasancewar sa dama nadi ne aka yi masa na siyasa, ba takamaimen ma’aikacin gwamnati ba ne.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa mai ba Gwamnan Kaduna Shawara a fannin ingata harkokin matasa, ta gayyaci ‘yan takarar uku zuwa ofishin ta, inda bayan ta tabbatar musu cewa gwamnati ba ta goyon bayan kowa a cikin su, sai ta gabatar musu da wata takardar da ke dauke da sunayen su, kuma ta ce kowa ya sa hannu a kan takardar, cewa ya yi alkawarin ba zai haddasa tarzoma ko wani rikici, kafin da kuma bayan zabe ba.

Daya daga cikin ‘yan takarar ya tabbatar mana faruwar haka, inda kuma ya ce kafin su shiga ofishin sai da aka kwace wayoyin kowanen su bayan an caje su. Dama kuwa kowa ya je da wasu daga cikin na hannun damar sa a wajen kamfen.

Jami’ar ta bayyana musu cewa su na da rahoton jami’an tsaro da ke hasashen cewa wani ko wasu daga cikin ‘yan takarar zai yi amfani da matasa ‘yan baberiya domin a yamutsa harabar zaben, zargin da kowanen su ya musanta.

Yayin da ake kallon Lere a matsayin rikakken dan adawar gwamnatin jihar Kaduna, shi kuma Al-amin an yi masa kallon makiyin gwamnatin jihar Kano.

Ganin yadda Ciroma ke da goyon bayan wakilan zabe da dama, an yi mamakin yadda ya fadi zaben kuma aka yi masa mummunar rata. Sai dai kuma bayan kammala zaben wata kwakkwarar majiya a Kano, ta shaida Premium Times Hausa cewa ba abin mamaki ba ne ba shi idan Ciroma ya fadi zaben.
Majiyar ta ce akwai da yawan masu ruwa da tsakin harkar fim wadanda ba su ji dadin yadda ya rika yin rubuce rubuce ya na sukar MOPPAN ta jihar Kano, dangane da dakatar da Rahma Sadau daga harkar fim da aka yi ba.

Wasu sun yi zargin cewa su na gudu kada bayan zaben sa ya ce ya soke dakatarwar da aka yi wa Rahma.

Hausawa na cewa bayan tiya, akwai wata caca. Tun ranar Juma’a da rana sai labari ya rika yawo cewa an ga wasu jami’an gwamnatin jihar Kaduna su na gilmawa a cikin harabar Otel din Royal Tropicana, inda aka tsara cewa a nan za a yi taro. Wata majiya kuma ta ce a Otel din Ni’ima su ka sauka musammam. Sai dai kuma sun shaida wa ‘yan fim din da suka san su cewa ba zaben ya kai su Kano ba, sun he yin wani sha’ani ne na daban.

Akwai alamomin da suka rika nuna cewa wasu manyan harkokin finafinai sun fi karkata a kan Abdullahi Maikano.

Babbar matsalar kungiyar MOPPAN a yanzu dai biyu ce. Na farko dai wannan gidan jarida ta ji daga kwakkwarar majiya cewa ko naira dubu goma babu a asusun kungiya har zuwa ranar zabe. Sannan kuma akwai matsalar shawo kan magoya bayan ‘yan takara. A fili ta ke cewa makusantan Al-amin Ciroma sun fusata sosai, kuma wasun su sun yi zargin cewa a daren da za a fara jefa kuri’a an canja wa wasu ‘yan takara ra’ayin wanda za su zaba.

Jerin Sunayen Shugabannin MOPPAN Na Kasa

1. Shugaba:
Abdullahi Maikano
2. Mataimaki Na 1.
Salisu Mu’azu
3. Mataimaki Na 2.
Nasiru B. Muhammad
4.Mataimaki Na 3.
Adamu Jahun
5. Sakatare Na Kasa:
Ahmed Alkanawy
6. Mataimakin
Sakatare:

Abdullahi Dan Asabe
7. Ma’aji:
Nura Hussaini
8. Jami’in Hulda Da Jama’a:
Maikudi Cashman
9. Sakataren Kudi:
Bello Achida
10. Sakataren Shirye-shirye:
Ahmed Hashim
11. Mai Binciken Kudi 1:
Haruna Goodwill
12. Mai Binciken Kudi 2:
Tijjani Faraga

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button