Friday, 12 May 2017
Neman Tsige Sarkin Kano Zai Taba Darajar Sarautu - Bafarawa

Home Neman Tsige Sarkin Kano Zai Taba Darajar Sarautu - Bafarawa
Ku Tura A Social Media
NEMAN TSIGE SARKIN KANO ZAI TABA DARAJAR SARAUTU- Bafarawa

Daga Ibrahim Baba Suleiman 

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce daukar sabbin matakai kan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bayan sulhun Kaduna ba daidai ba ne.

Bafarawa da ke magana da manema labaru a Abuja, ya ce karin mataki ko ma neman kwabe Sarkin zai rage darajar sarauta ne da hadin kan arewa.

Yayin da Bafarawa ke ganin sulhu ne mafi a'ala, ya ce ba wai ya na kare Sarkin ba ne, amma ya na kare kujerar sarautar ce da ke da tasiri wajen hadin kan al'umma.

Sakkwato Birnin Shehu 
12th May, 2017

Share this


Author: verified_user

0 Comments: