Tuesday, 23 May 2017
Matashin yaro daga Adamawa ya ci 308 a jarrabawar JAMB ta 2017 (DUBA)

Home Matashin yaro daga Adamawa ya ci 308 a jarrabawar JAMB ta 2017 (DUBA)
Ku Tura A Social Media

- Wani matsahin yaro daga jihar Adamawa ya ci maki 308 a jarrabawar shiga jami’a

- Bashar Umar Shagari, wani mai amfani da shafin zumunta, ya buga a shafin Facebook don ya taya yaron mai kwazo murna

Wani matsahin yaro daga jihar Adamawa, Abdulrahman Ali ya ci maki 308 a jarrabawar shiga jami’a wato Joint Admission Matriculation Board (JAMB) wanda aka kammala kwanan nan.

Wani mai amfani da shafin zumunta, Bashar Umar Shagari ya buga a shafin Facebook don ya taya yaron mai kwazo murna, tare da taken:
Hazikin yaron da ya ci 308 a JAMB daga AdamawaHazikin yaron da ya ci 308 a JAMB daga Adamawa

“Dole Gwamna Bindow ya ga wannan sannan kuma na jinjina ma gwarzon shekara. Abdulrahman Ali daga jihar Adamawa, wanda ya ci 308 a jarrabawar JAMB 2017, ina taya ka murna yaro, ina ma ace na kai ga cin wannan maki a lokacin da na rubuta nawa jarrabawar.”

©Naij.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: