Tuesday, 2 May 2017
Dalilin da yasa MTN ta sallami ma’aikata 280

Home Dalilin da yasa MTN ta sallami ma’aikata 280
Ku Tura A Social Media

Kungiyar kwadago a Najeriya ta yi allawadai da korar daruruwan ma’aikata da kamfanin sadarwa na MTN ya yi.

MTN ya sallami tsoffin ma’aikatansa da masu kwantaragi kusan 300, wato kashi 15 na yawan ma’aikansa a Najeriya.

Mafi yawa daga cikin wadanda kamfanin ya korar sun shafe shekaru 15 suna masa dawainiya tun lokacin da ya soma aiki a Najeriya ciki shekara ta 2001.

Majiyoyi sun shaida cewa korar ma’aikatan ya biyo bayan sauye-sauye da ake samu a harkokin sadarwa na wannan zamani.

Tuni dai kungiyoyin kwadago a Najeriya suka soma sukar wannan mataki da MTN ya dauka.

Sources:rfihausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: