Thursday, 23 February 2017
Yayin Da Allah Ya Halicci Aljannah Da Wuta - Dr Sheikh Muhammad Sani Umar R/Lemo

Home Yayin Da Allah Ya Halicci Aljannah Da Wuta - Dr Sheikh Muhammad Sani Umar R/Lemo
Ku Tura A Social Media
Yayin Da Allah Ya Halicci Aljanna Da Wuta!

“Lokacin da Allah ya halicci Aljannah, sai ya ce wa Mala’ika Jibrilu, ‘Jeka ka ganta’. Yayin da ya je ya ganta, sai ya dawo ya ce wa Allah, ‘Ya Ubangijina! Na rantse da izzarka, babu wanda zai ji labarin Aljannah, sai ya yi kokarin ya shige ta’. Sai Allah ya kewaye ta da abubuwan da rai ba ta so, sannan ya ce, ‘Ya Jibrilu! Je ka yanzu ka ganta’. Da ya je ya ganta, sai ya dawo ya ce, ‘Ya Ubangijina! Na rantse da izzarka, ina tsoron yanzu kam babu wani wanda zai iya shigarta’.

 Yayin da kuma ya halicci wuta, sai ya ce, ‘Ya Jibrilu! Je ka ka ganta’. Da ya je ya ganta, sai ya dawo ya ce, ‘Ya Ubangjijina! Na rantse da izzarka, babu wani da zai ji labarinta, sannan ya yarda ya shige ta’. Sai Allah ya kewaye ta da abubuwan sha’awa, ya ce, ‘Ya Jibrilu, je ka yanzu ka ganta’. Da ya je ya ganta sai ya dawo ya ce, ‘Ya Ubangijina! Na rantse da izzarka, babu wani wanda zai rage bai shige ta ba’..”. [Ahmad, #8648, Daga Abu Hurairah (R.A.)].

Share this


Author: verified_user

0 Comments: