Uncategorized

Mulki Baya Dorewa Sai Da Abu Biyu!!!- Sheikh Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

Mulki Baya Dorewa Sai da Abu Biyu:

Mulki baya kafuwa ya yi karko ya dore sai da abubuwa biyu:

Na Farko: JARUMTA ,Wadda itace,hukunta duk wani mai laifi ba sani-ba -sabo,Wanda yin hakan Zai jefa Tsoro a Zuciyar da wani mai shirin yayi barna.

Na Biyu: KARAMCI,Wanda yake nufin kyautatawa da ihsani ga duk Wani Wanda ya cancanci  kyautatawa da ihsani saboda kyawawan Ayyukansa da kwazonsa.

Yayin da aka rasa wadannan abubuwa biyu ko aka rasa daya daga cikinsu to mulki ba zai dore ba,ko kuma bazai kyau ba.

Dubi JARUMTAR Zul-kKarnaini,inda yake cewa ,”To amma wanda yayi Zalunci,to zamu Azabar da shi ,yi masa Mummunar azaba.”[Al-kahfi,87]

Sannan dubi KARAMCINSA, A Maganarsa da yake cewa,”Amma kuma duk Wanda Yayi Imani,kuma yayi aiki na gari ,to yana da kyakkyawan sakamako,kuma za mu fada masa tattausar magana game da al’amarinmu.”[Al-kahfi,88]


Allah ka baiwa shuwgabaninmu wanannan abubuwa guda biyu ,domin su zamo masu amfani da ayoyin Allah.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button