Friday, 20 January 2017
FATAWAR RABON GADO 93 DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO 93 DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
*FATAWAR RABON GADO 93*

*_Tambaya:_*
Salam Alaikum, Allah ya karama malam lafiya amin. Ina da tanbaya akan gado. Malam mahaifiyace ta rasu tabar mijinta da mahaifiyarta, da kaninta da yarta sannan da yara takwas maza biyar mata uku. Ya rabon gadonta zai kasance. Nagode. 

*_Amsa:_*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida sha biyu: a bawa mahaifiyarta kashi biyu (Sudus), sai a bawa mijinta kashi uku (Rubu'i), Ragowar kashi bakwan sai a bawa 'ya'yanta su raba duk namiji ya dau rabon mata biyu. 

'Yan'uwa ba sa gado mutukar a 'ya'yan mamata akwai namiji.

Allah ne mafi sani. 

✍🏼 Amsawa:
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
18/1/2017

posted  Abubakar Rabi'u

Share this


Author: verified_user

0 Comments: