FATAWAR RABON GADO (91)| DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (91)*

*Tamabaya*
Assalamu akaikum malam,
MACE CE TA MUTU TA BAR DA NAMIJI GUDA DAYA DA MAHAIFIYARTA DA KUMA MIJIN TA. malam don Allah yaya robon gadon ta zai kasance ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, za'a raba abin da ta bari gida 12, sai a bawa mijinta kashi uku, mahaifiyarshi kashi biyu, ragowar sai a bawa danta.  
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
6/1/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment