Friday, 6 January 2017
FATAWAR RABON GADO (90) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO (90) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media

*FATAWAR RABON GADO (90)*

*Tambaya*
Assalamu alaikum malam, wasu ne suke cikin wani rikici a rabon gado shi ne muke so a raba mana: mace ce ta rasu ta bar mijinta da mahaifanta da danta da yarta ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida:24, sai a bawa mijinta kashi shida (rubu'i), Mahaifiyarta kashi hudu (sudus), mahaifinta kashi hudu (sudus), sai a bawa 'ya'yanta biyu ragowar kashi goman su raba gida uku, namiji ya dau kashi biyu macen ta dau kashi daya.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*
5/1/2017

Share this


Author: verified_user

0 comments: