Thursday, 5 January 2017
FATAWAR RABON GADO (89) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO (89) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
FATAWAR RABON GADO (89)
Tambaya?
Assalamu alaykum wa rahmatulLahi wa barakatuh.Allah Ya qara wa Mallam sani,tambaya ce gare ni dangane da rabon gado.Mutum ne ya mutu ya bar uwa da 'yan uwa shaqiqai guda shidda-maza 4,mata 2.Bai bar diya ba da mata,ya rabon gadon sa ya ke?
Amsa :
Wa'alaykumussalam,
za'a raba abin da ya bari gida : 6, a bawa mahaifiyarsa kashi daya, Ragowar kashi biyar din sai a bawa yan' uwan shakikai, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani.
3/1/2017
DR JAMILU ZAREWA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: