Uncategorized

FATAWAR RABON GADO (88) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (88)*

*_Tambaya:_*
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu,
Malam Da fatan kana lafiya, don Allah Malam ga Tambayata kamar Haka:
Wani kaninane Ya Rasu Ba shi da ‘Da Bashi da mata sai Mahaifiya da ‘yan uwa wadanda suke uwansu daya uba daya, maza biyu mata biyu, sai kuma wanda Suka Hada uwa kawai, namiji daya mace daya to ya ya za a raba musu Gadon da ya Bari?.
*_Amsa:_*
Wa alaikum assalam, za a raba abin da ya bari gida: 6, sai a bawa mahaifiyarsa kashi daya, ‘yan’uwan da suka hada uwa daya kawai kashi biyu, Za su raba daidai babu bambanci tsakanin namiji da mace, ragowar kashi uku sai a bawa ‘yan uwansa shakikai, Duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani.
✍ Amsawa:
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
28/12/2016.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button