FATAWAR RABON GADO (87) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (87)*

*_Tambaya:_*
Assalamu alaikum, Malam ina da tambaya Don Allah, Mata ta  mutu ta bar diya mace daya, da iyayenta uwa da uba, da mijinta, ya za'a raba abinda ta bari?.
*_Amsa:_*
Wa alaikum assalam, Za a  raba abin da ya bari gida:13, (Auli daga 12) a bawa 'ya mace kashi:6, uwa kashi:2, Uba kashi:2, sai kuma a bawa miji kashi uku.
Allah mafi sani
✍ Amsawa:
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
26/12/2016

Share this


0 comments:

Post a Comment