Uncategorized

ALLAH NA TSARE ‘YA’YA SABODA KIRKIN MAHAIFINSU. DR MUH’D SANI UMAR R/LEMO

ALLAH NA TSARE ‘YA’YA SABODA KIRKIN MAHAIFINSU.

Idan bawa ya zama mai kirki,ya gujewa bin son zuciya,Allah yana tsare masa zurriyarsa bayan rasuwarsu ,ya tsare masa su daga sharri da tozarta.
Dubi yadda Allah ya tsare  dukiyar wadannan marayu da khadir (A.S) ya mikar garu saboda dukiyarsu da take karkashinsa,don gudun kada ya fadi mutanen gari su kwashe musu dukiyarsu.

ALLAH  ya ba mu labarin hakan,inda yake cewa ,”To amma dangane da wannan garun,ya kasance na wasu yarana ne marayu a cikin garin,a karkashinsa kuwa akwai wata taska tasu,mahaifinsu kuma ya kasance mutumin kirki ne,to sai ubangijinka ya nufi su kai ganiyar karfinsu, su fito da taskarsu don rahma daga ubangijinka .[Al-kahfi,82].

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button