Monday, 5 December 2016
KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
*KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! !*

*Tambaya*

Assalamu alaikum mal dan Allah ga tambaya nan
Nice nai aure na ya rabu da mijina, wato ya bani takardan saki, kafin ya bani wannan takardar,mun samu matsala na bar gidanshi tsawon shekara daya da wata tara,kuma Daman tsawon zaman mu tare shekara bakwai ban taba samun ciki ba,yaya iddata zata kasance ?

*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za ta jira tsarki uku, tun da sun taba kawanciyar aure kamar yadda aya ta 228 a Suratul Bakara  ta tabbatar da hakan.
                                                               Hukunce-hukuncen Saki suna farawa ne daga lokacin da aka yi saki, ba daga sanda aka samu hatsaniya ba.                          Allah ya shar'anta idda saboda manufofi da yawa daga ciki akwai: bawa miji damar kome Idan saki daya ne ko biyu, ta yiwu wani daga cikin ma'aurata ya yi nadama, Tare da cewa babban makasudin shi ne tabbatar da kubutar mahaifa, Amma ba shi kadai ba ne.
Allah ne mafi sani

*Amsawa*
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*
25/11/2016

Share this


Author: verified_user

0 Comments: