Monday, 5 December 2016
HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media

HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA ! !


Tambaya?

Assalamu Alaikum! Mallam ina tambaya idan mutum  ya sadu da matarsa tana haila me ya kamata yayi?,  kuma ina neman cikekken bayani mallam.

Amsa :

Wa alaikum assalam,
Wanda ya sadu da matarsa tana haila, ya wajaba ya yi istigfari saboda ya aikata abin da Allah ya hana a aya ta: 222 a suratul Bakara, Wannan ita ce maganar mafi yawan malamai kamar yadda Ibnu Rushd ya fada a Bidayatul mujtahid.
                    
Hadisin da ya zo na cewa: (Wanda ya sadu da matarsa tana haila ya yi sadaka da rabin dinare) bai inganta ba, wannan yasa ba za'a iya gina hukunci akansa ba.
Allah ne mafi sani
27/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: