Tuesday, 20 December 2016
FATAWAR RABON GADO (83) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO (83) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
FATAWAR RABON GADO (83)

Tambaya?
Assalamu alaykum Warahmatullah wabarakatuh.
Malam inada tambaya ne ataimaka man da amsar ta don Allah, tambayar itace kan gado mutum ne ya rasu baiyi aureba yabar mahaifiya, da ya'ya mace uba daya, sai kanwa da suka hada uba daya, sai kannai maza da mata da suka hada uwa daya, to yaya gadon zai kasance. Allah yakara basira a huta lafiya.

Amsa :
Wa alaikum assalam,
Za'a raba abin da ya bari gida: 7, (Auli daga:6) sai a bawa Mahaifiyarsa kashi daya, 'yar'uwansa mata da suka hada uba daya kashi hudu, :4, 'yan'uwansa da suka hada uwa daya kawai kashi biyu.
'ya'yan uwa za su raba abin tsakaninsu, babu bambanci tsakanin namiji da mace.
Allah ne mafi sani.
5/12/2016
DR JAMILU ZAREWA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: