Tuesday, 20 December 2016
FATAWAR RABON GADO (82)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO (82)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
FATAWAR RABON GADO (82)

Tambaya?
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu
Tambaya akan rabon gado.
Yaya Rabon gadon matar da ta mutu ta bar Mijinta, da uwatta da ubanta da kuma yan uwanta shakikai da li'abbai da li'ummai?
Allah ya bada ikon taimakawa.

Amsa :
Wa alaikum assalam,
Za'a raba abin da ta bari kashi shida, a bawa mijinta kashi uku, banbanta kashi biyu, mahaifiyarta kashi daya.
Allah ne mafi sani.
2/12/2016
DR JAMILU ZAREWA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: