Wednesday, 23 November 2016
MENENE HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home MENENE HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
M
ENENE HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA ?

Babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai sun yi sabani a cikin mas'alar zuwa maganganu guda uku:wacce ta fi inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da juma'a guda daya a gari daya, mutukar akwai bukatar hakan, kamar ya zama masallacin farkon ba zai ishi mutane ba, ko kuma za'a samu wata fitina idan aka hadu wuri daya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala,

wajan isowa zuwa gare shi, idan babu bukata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda daya a gari daya, saboda daga cikin hikimomin shar'anta juma'a akwai samun hadinkan musulmai, hakan kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda daya,

wannan itace maganar Ibnu Taimimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu manyan maluma Allah ya yi musu rahama. 

Amsawa Dr.jamilu zarewa

posting by Abubakar Rabiu Yari

Share this


Author: verified_user

0 Comments: