Tuesday, 4 October 2016
Za a kaddamar da sabon kwamiti nazarin zabe a Najeriya

Home Za a kaddamar da sabon kwamiti nazarin zabe a Najeriya
Ku Tura A Social Media
A wannan talatar ake saran kaddamar da wani sabon kwamiti a Najeriya da zai yi nazari kan dokokin zaben kasar ya kuma bada shawara kan yadda za a inganta su dan samun zabe mai sahihanci a kasar.
Kwamitin zai yi aiki ne a karkashin tsohon shugaban Majalisar Dattawan kasar, Ken Nnamani.
Wannan dai ba shine karo na farko ba da ake kaddamar da irin wannan kwamiti, ganin na Justice Mohammed Lawal Uwais da ya yi irin wannan aikin bada dadewa ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: