Friday, 14 October 2016
Yan jam’iyyar APC 6000 sun sheke PDP

Home Yan jam’iyyar APC 6000 sun sheke PDP
Ku Tura A Social Media
A kalla yan Jam’iyyar APC 6000 sun sheke PDP a karamar Hukumar idanre a jihar Ondo
– Wadanda suka sheke sunce sunyi hakan ne saboda soyayyar da suke wa dan takaran gwamnan Eyitayo Jegede
– Sun ce dan takaran APC, Rotimi Akeredolu bashi da shaharan cin zabe
Jaridar Sun ta bada rahoton cewa akalla mambobin APC 6000 ne suka sheke jam’iyyar PDP a jihar ondo a ranan Alhamis, 13 ga watan Oktoba.

Wadanda suka sheke sunce sunyi hakan ne saboda soyayyar da suke wa dan takaran gwamnan Eyitayo Jegede.
Jagoransu Adebowale Olowoeye, ya ce sun sha alwasin goyan bayan Eyitayo Jegede a zabe kuma sun alanta taimakawa jam’iyyar a zaben da za’a yi.
An tattara cewa a yankin Ofosu Onisere kadai , mutane 86 ne suka sheke PDP. Kana mutanen Ala 1000 ne suka bar jam’iyyar APC.
Yayinda ake musu maraba zuwa jam’iyyar, wakilin gwamnan, Kola Ademijimi yace goyan bayan da mutane ke baiwa gwamnatinsa nada kyau.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: