Friday, 7 October 2016
Najeriya ta gabatar da kudirin janye karar Saraki a Kotu

Home Najeriya ta gabatar da kudirin janye karar Saraki a Kotu
Ku Tura A Social Media
Gwamnatin Najeriya ta gabatar da kudiri a gaban kotun da ke Abuja na janye karar da aka kai shugaban Majalisar Dattawan Bukola Saraki da Mataimakin sa na sauya dokokin Majalisa.

Wani jami’in ma’aikatar shari’ar kasar Odubu Loveme ya gabatar da takardar janye karar a gaban kotun ranar Alhamis.
Ita dai gwamnatin ta zargi Bukola Saraki da mataimakin sa Ike Ekweremadu da kuma tsohon kakakin majalisa Salisu Maikasuwa da mataimakin sa Ben Etifuri da sauya dokokin zaben da ya bai wa Saraki damar hawa kujerar shugabancin Majalisar.
Su dai wadanda ake zargin sun ki amincewa da tuhumar a shari’ar da ta dauke hankalin 'Yan Najeriya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: