Saturday, 22 October 2016
Mutane 53 sun rasa rayukansu a hadarin Jirgin kasa

Home Mutane 53 sun rasa rayukansu a hadarin Jirgin kasa
Ku Tura A Social Media
Mutane 53 sun rasa rayukansu a hadarin Jirgin kasa
Hadarin Jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa Yaounde
Rahotanni daga kasar Kamaru sun ce akalla mutane 53 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin jirgin kasa.
Jirgin fasinjan yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Yaounde daga Douala, a lokacin da ya kauce daga kan titinsa.
Kafin wannan hadari dai, wata gada da ke hada cibiyar hada-hada da ke hada Douala da Yaounde ta karye, hakan yasa mutane zabin shiga jirgin kasa.
Shaidun gani da ido sun ce yawan da jama’a suka yi cikin jirgin ya taimaka, wajen sabbaba aukuwar hatsarin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: