Sunday, 30 October 2016
FATAWAR RABON GADO (69)|DR JAMILU ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO (69)|DR JAMILU ZAREWA
Ku Tura A Social Media
FATAWAR RABON GADO (69)
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam don girman Allah a taimake ni da Amsan tambaya ta kamar haka :
Mace ce ta mutu bata da iyaye ba Da ba jika sai qanwarta guda daya shaqiqiya sai kuma li'abbai guda biyar biyu maza uku mata.  Ya za'ayi rabon gadon ta?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida 2, sai a bawa shakikiyar  rabi, ragowar kuma sai a bawa li'abban su raba a tsakaninsu, duk namiji zai dau RABON mata biyu.
Allah ne mafi sani
25/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: