Uncategorized

Wasu abubuwa 13 da suka sauya a Najeriya daga 1960

Najeriya ta samun yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekara 1960, daga lokacin zuwa yanzu, tsawon l

okacin zuwa yanzu da akwai abubuwa da yawa da suka canza a kasar, ga wasu 13 daga cikinsu.

Firayi minstan Nigeria na farko Tafawa Balewa tare da Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto kuma Firimiya Arewa
1.Salon mulki: Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka canza a Najeritya tun lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai. A waccan lokaci Najeriya na bin salon mulkin ‘Parliamentary’ ne irin na Britaniya, a inda Firayi Minista ne ke da wuka da kuma nama a gudanar da mulki, yanzu kuwa kasar ta sauya zuwa ga tsarin shugaba mai cikakken iko irin na Amurka, watau ‘Presidential’.
2.Canjin kudi: Wani a muhimmin al’amari da ya sauya a Najeriya shi ne sauyin kudin kasar daga Fam da zuwa Naira da Kwabo a shekarun 1970.
3.Lissafin mita-mita: An koma lissafin mita-mita a maimakon mil-mil a nisan tafiya. Nisan gari zuwa gari daga mil ya koma kilomita da dangoginsa, hankan ya sauya lisssafin a kasar.
4.Tuki ya koma dama: Haka ma fasalin tuki a kasar ya sauya daga hagu wanda aka gada daga turawan mulkin mallaka zuwa dama.
5.Juyin mulki na farko: wani babban al’amari da ya faru a tarihi kasar shi ne shigar sojoji harkar siyasa bayan da wasu sojojin suka yi juyin mulki na farko a shekara 1965, a inda aka hallaka shugaban gwamnatin kasar da wasu manya-manya daga arewa da kuma kudu. Da wannan yunkuri soja a kasar suka dandana mulkin siyasa.
Tashin hankali lokacin yakin basasan Najeriya
6. Yakin Basasa: Kokarin da ‘yan kabilar Igbo suka yi na ballewa daga Najeriya ya haifar da yakin basasa a shekarun 1965 zuwa 1970, wanda hakan ya sauya yadda sauran kabilu ke kallon ‘yan kabilar Igbon da ma sauran kabilun kasar ta fuskar mu’amilla da zamantakewa.
7.Ayyukan Noma: A lokacin da Najeriya ta samu ‘yancin kai noma ne ke rike da kasar, kudu na fitar da Koko, da kwakwar manja, arewa kuma na fitar da fata, da gyada, da shanu da sauransu zuwa kasahen waje, a yanzu kuwa abin ya sauya, a yayin da kasar ce ke shigo da abinci.
8.Man fetur: Gano man fetur a kudu ‘yan  kadan bayan samun ‘yancin kai, ya sa kasar ta zamo mai arziki, hakan kuma ya sa abubuwa da yawa sun sauya, ciki har da hali da kuma dabi’un ‘yan kasar.
9.Sabbin jihohi: Janar Murtala ne ya fara kirkiro jihohi 12 a shekarun 1970, daga yakuna hudu da ake da su a shekarun 1960. Babangida kuma ya kara yawansu a shekarun 1990, wadannan sauye-sauye sun canza fasalin kasar matuka.
10.Abuja: Fadar gwamnatin tarayya ta tashi daga Legas da aka saba tun karbar yancin kai, zuwa Abuja, wani wuri na daban a tsakiyar kasar, hakan ya sauya alkiblar ‘yan kasar ta hanyar gudanar da mulki.
11.Bunkasar birane: Manyan garuruwa a shekarun 1960 ba su da yawa, amma a yanzu sakamakon kirkiro jihohi da habbakar tattalin arziki, an samu wasu garuruwan da a shekarun 1960 kauyuka ne, amma a yanzu sun zama kayatattun birane, sun kuma shahara.
12.Kimiyya da fasaha: A shekarun 1960 babban ma’aikacin gwamnati ko attajiri ne za iya sa waya a gidansa, amma a yanzu da sauyin na fasaha da kimiyyar zamani musamman ta fusakar sadarwa kowa ya wadata da wayoyin hannu na wadanda ke taimakawa gudanar da rayuwa cikin sauki.
13.Yawan tashe-tashen hankula: Harkokin siyasa, da na kabilanci, da na addinai sun yi tasirin da kwanciyar hankali ya yi karanci a yanzu, ba kamar a shekarun 1960 ba, a inda ake zaune lafiya da kwaciyar hankali.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button