Sunday, 25 September 2016
FATAWAR RABON GADO (56)|Dr.Jamilu yusuf zarewa

Home FATAWAR RABON GADO (56)|Dr.Jamilu yusuf zarewa
Ku Tura A Social Media
FATAWAR RABON GADO (56)
Assalamu alaykum.
Malam inada tambaya? Allah gafarta malam, shin idan mace ta rasu batada miji da iyaye sai '' ya'ya uku mata batada namiji, shin '' yan uwanta da suke uba daya sunada gadonta?
Amsa :
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari kashi uku, sai a bawa 'ya'yanta kashi biyu, ragowar kashi dayan sai a bawa 'yan'uwanta da suka hada uba daya in har babu shakikai.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
19/Dhul-Hijjah /1437
21/09/2016

Share this


Author: verified_user

0 Comments: