Saturday, 27 August 2016
Rancen Airtime na Mtn ba Riba ce ba|Dr. Muhd sani umar R|lemo

Home Rancen Airtime na Mtn ba Riba ce ba|Dr. Muhd sani umar R|lemo
Ku Tura A Social Media

Dr. Muhd Sani Umar R/lemo

Rancen Airtime Na Mtn Ba Riba Ce Ba:

A Azumin bara (1436H) an mini tambaya game da bashin da kamfanin Mtn yake ba wa masu mu’amala da shi. Ka ranci airtime na misalin N50, a ba ka na N45. A karon farko na bayar da amasar cewa, Haramun ne! Kuma zai shi ga babin ribal Qardh!. Daga baya na janye wannan fatawar saboda yadda na kara fahimtar mas’alar, na ba da fatawar halaccin ta, saboda dalilai kamar haka:
1. Wannan mas’ala ba bashi ne na kudi da kudi ba, ballantana batun ribal Kardh ta zo.
2. Abin da yake hakikanin mas’alar shi ne, wani ne mai amfani ne da wannan kamfani na Mtn ya sayi hidima ta aritime (airtime service) wadda suke sayar da ita N45, sai suka sayar masa ita a N50.
3. Kasancewar an ambaci kudi a cikin ciki ba shi yake tabbatar da cewa kudi da kudi ne aka yi musanyan su ba. An yi musanyan kudi ne da wata hidima (airtime service) wanda masu ita suka ki ba shi ita a farashin da suke sayar da ita kudi hannu, suka kara masa wani abu akai. Wannan ba komai ne ba a shari’ance ba, saboda kayansu ne, suna da damar su yi maka kari kamar yadda suke da damar su yi maka ragi, kuma ka karba.
4. Abin da zai tabbatar maka da cewa, wannan abin da ka nema su ba ka ba tsurar kudi ne ba, hidima ce kawai, wanda aka bas hi ita a wayarsa ba za iya sayen komai da wannan ba a gurin wani ya ce yana da kudin biya a gurinsa, a she ka ga ba kudi ne ba, koda an rubuta alamar kudi a tare da shi.
5. Kamar yadda ya halatta katin waya na N100 a sayar wa da mai bukata akan N110, duk da cewa ga shi a rubuce an rubuta N100. Ko a sayar masa da shi N95, wanda babu wani masani da ya taba cewa, wannan riba ce ko haramun ne, saboda musanyar kudi da kudi ne. Domin alala hakika wannan katin wayar mai dauke da N100 a kansa ba kudi ne ba, wata hidima ce, aka yi mata ramzi da wannan 100, shi ya sanaya da zarar ka kankare ka shigar ita cikin wayarka zaka jefar da wannan katin tare da cewa an rubuta kudi a jiki, To wannn masa’al ta rance kamar haka take, don haka, duk wanda ya harmta wannan to wajibi ya haramta sana’ar sai da kati. Wanda ban a jin akowa mai fadar hakan.
6. Don haka ba magana ce ta an ba ni fatawa a baibai ba, magana ce ta sake nazari akan fatawar farko, wanda wannan abu ne sananne a gurin manyan malamanmu magabata da suke canza fatawoyinsu yayin da wasu dalilai suka bayyana gare su.
7. Wannan matsaya kuma shi ne matsayar wasu daga cikin abokai na daliban ilimi bayan sun kalli mas’alar ta mahanga lilimi da sanin abin da ake kira riba, daga cikinsu akwai abokina Dr. Bashir Aliyu Umar kamar yadda daga baya na samu labari.
8. Daga karshe ina kira ga sauran ‘yan uwana diliban ilimi mu yi kaffa-kaffa wajen sakin baki game da sha’anin halal da haram, al’amarin yana da hadari. sanin madafar shari’a ta wanda ya karanta ta ne. Allah ya sa mu dace. Amin.

Sheaik Dr Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo

Share this


Author: verified_user

0 comments: