FATAWAR RABON GADO (49)|Dr.jamilu zarewa

FATAWAR RABON GADO (49)
Tanbaya?
Assalamu alaykum malam ina da tambaya. Magidanci ne ya rasu. ya bar  Yara 12, maza 8 mata 4 da kuma iyalinsa. Biyu, uwargida tana da Yara 9 amarya tana da Yara 3, to amarya ta yi aure, ya rabon gadon chike?, Allah chi karama malan lafiya amin
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida:8, a bawa matansa kashi daya su raba, ragowar kashi bakwan sai a bawa 'ya'yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani.
Amsawa Dr Jamilu Zarewa
22 /08 /2016

Share this


0 comments:

Post a Comment