Thursday, 18 August 2016
BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?

Home BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?
Ku Tura A Social Media
BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?
Tambaya?
Assalamu Alaikum.
Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo.                                                                               Aya ta biyu a cikin suratul Ma'ida tana cewa: "Kuma ku dinga tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata sabo".                                                Ibadar COCI shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma'ida suka siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri.       
Allah Ne mafi Sani.
Dr Jamilu Zarewa
16/08/2016

Share this


Author: verified_user

0 comments: