Uncategorized

IDAN MASABUKI YA RISKI LIMAN A RAKA’A TA BIYAR YA SAMU JAM’I?

IDAN MASABUKI YA RISKI LIMAN A RAKA’A TA BIYAR YA SAMU JAM’I ?

Tambaya:

Assalamu alaikum,
Akramakallahu idan liman ya yi kuskuren kara raka’a daya, masbukin da aka tsere ma da rakaa daya za ta ishe shi idan Anyi baadiyya tare da shi?

Amsa:

Wa alaikum assalam, Allah ya taimaki shehinmu, malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa zantuka biyu :

Akwai wadanda suke ganin za ta isar masa.

Sai dai abin da na fi nutsuwa da shi a raina, shi ne ba za ta isar masa, saboda mamu sallarsa tana like  da ta liman ne, shi kuma liman ya zo da raka’ar a kuskure, wannan ya sa kamar yadda ba za ta amfani liman ba, haka ba za ta amfani mamu ba, wannan ita ce fatawar Sheik Ibnu Bazz da Sheik Abdulmuhsin Al-abbad.

Yana daga cikin ka’idojin sharia: mabiyi ba ya kebanta da hukunci.            

Allah ne mafi sani.
                                                                          

       Dr Jamilu Zarewa.                                                                                         23 Ranadhan 1437

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button