Thursday, 2 June 2016
A LOKACIN DA GWAMNA AMINU WAZIRI YAKE RANTSAR CIYAMOMI 22An yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da su yi takatsantsan da kudaden alumma a lokacin gudanar da mulkin su. Gwamnan jahar sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal CFR ne yayi wannan kiran alokacin da yake rantsarda shugabannin kananan hukumomin jahar su 22. Tambuwal yace kowannen su zai yi bayanin yadda ya tafyar da mulkin sa agaban ubangiji, ya bayyana cewa gwamnati ta sa an gudanar da binciken maikata na kowane bangare don tantance maikatan a tabbata wadanda za a kula da su kuma anci nasara akai. Yace duk da cewa ana fama da kalubalen tattalin arziki yana da kyau su yi amfani da abun da suke da wajern kawo ci gaba mai ma'ana a kananan hukumomin su. Ya bayyana cewa ci gaban ba zai samu ba sai ciyamomin sun hada hannu da uwayen kasar su,kansiloli da maaikatan karamar hukumar baki daya,kuma kofarsu ta zamo bude ga alumma a ko yaushe. Hakama yayi kira gare su dasu bada gudun muwarsu ga samun ci gaban wanzuwar damokradiyya ta hanyar zama shugabanni na gari abin koyi.Gwamnan yace an gudanar da zaben ciyamomin cikin kwanciyar hankali da adalci ta hanyar amfani da naurar tantance masu zabe wanda akai yi a gaban kungiyoyi daban daban masu sa ido sun kuma gamsu da abun da suka gani, in banda zaben karamar hukumar mulkin Gudu, da aka samu yan matsalolin da suka shafi lamurran zabe.Akan haka an rantsar da Engnr Maidamma Tangaza a matsayin kantoman da zai yi rikon kwarya a karamar hukumar kafin a yi zabe. Tambuwal yace wa ciyamomin su zama fadake da sanin cewa jama'arsu sun zabe su ne cike da gurin cewa zasu kawo musu abubuwan ci gaba a yankunansu ta hanyoyi daban daban. "kasancewa kanan hukumumomi zasu ci gaba da cin gashin kan su yana da kyau su ci gaba da sa ido ga lamurran maikatarsu don samun kyakkyawan shugabanci" in ji Tambuwal. Gwamnan yayi kira ga ciyamomin da su ba fannin Ilimi,Noma,karfafawa mata da matasa, lafiya,samarda ababen more rayuwa da na samarda kudaden shiga kulawar da ya kamata don ciyar da yankunan su gaba. Da yake magana kan tsaro gwamnan ya ce hakkin kowace gwamnati ne ta tabbatarda ana bin doka da oda don haka su tabbatar da suna yin taron tattaunawa dangane da shaanin tsaro a kanan hukumomin su kuma kulla kyakkyawar dangantakar aiki tsakanin su da masu aikin sarki(kaki) a yankunansu. Hakama yayi kira ga resu da su tabbatar su da maikatansu suna zuwa wurin aiki don gwamnati ba zata aminta da rashin zuwa aiki ba sai ranar albashi yace duk wanda aka sama da aikata hakan za a hukunta shi. Nan bada dadewa ba za a rarraba mukaman maikatan kananan hukumomi don bada damar gudanarda mulki yadda ya kamata. Ya godewa shugabanin rikon kwarya kan aikin da suka yi na watanni kafin a rantsar da ciyamom

Home A LOKACIN DA GWAMNA AMINU WAZIRI YAKE RANTSAR CIYAMOMI 22An yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da su yi takatsantsan da kudaden alumma a lokacin gudanar da mulkin su. Gwamnan jahar sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal CFR ne yayi wannan kiran alokacin da yake rantsarda shugabannin kananan hukumomin jahar su 22. Tambuwal yace kowannen su zai yi bayanin yadda ya tafyar da mulkin sa agaban ubangiji, ya bayyana cewa gwamnati ta sa an gudanar da binciken maikata na kowane bangare don tantance maikatan a tabbata wadanda za a kula da su kuma anci nasara akai. Yace duk da cewa ana fama da kalubalen tattalin arziki yana da kyau su yi amfani da abun da suke da wajern kawo ci gaba mai ma'ana a kananan hukumomin su. Ya bayyana cewa ci gaban ba zai samu ba sai ciyamomin sun hada hannu da uwayen kasar su,kansiloli da maaikatan karamar hukumar baki daya,kuma kofarsu ta zamo bude ga alumma a ko yaushe. Hakama yayi kira gare su dasu bada gudun muwarsu ga samun ci gaban wanzuwar damokradiyya ta hanyar zama shugabanni na gari abin koyi.Gwamnan yace an gudanar da zaben ciyamomin cikin kwanciyar hankali da adalci ta hanyar amfani da naurar tantance masu zabe wanda akai yi a gaban kungiyoyi daban daban masu sa ido sun kuma gamsu da abun da suka gani, in banda zaben karamar hukumar mulkin Gudu, da aka samu yan matsalolin da suka shafi lamurran zabe.Akan haka an rantsar da Engnr Maidamma Tangaza a matsayin kantoman da zai yi rikon kwarya a karamar hukumar kafin a yi zabe. Tambuwal yace wa ciyamomin su zama fadake da sanin cewa jama'arsu sun zabe su ne cike da gurin cewa zasu kawo musu abubuwan ci gaba a yankunansu ta hanyoyi daban daban. "kasancewa kanan hukumumomi zasu ci gaba da cin gashin kan su yana da kyau su ci gaba da sa ido ga lamurran maikatarsu don samun kyakkyawan shugabanci" in ji Tambuwal. Gwamnan yayi kira ga ciyamomin da su ba fannin Ilimi,Noma,karfafawa mata da matasa, lafiya,samarda ababen more rayuwa da na samarda kudaden shiga kulawar da ya kamata don ciyar da yankunan su gaba. Da yake magana kan tsaro gwamnan ya ce hakkin kowace gwamnati ne ta tabbatarda ana bin doka da oda don haka su tabbatar da suna yin taron tattaunawa dangane da shaanin tsaro a kanan hukumomin su kuma kulla kyakkyawar dangantakar aiki tsakanin su da masu aikin sarki(kaki) a yankunansu. Hakama yayi kira ga resu da su tabbatar su da maikatansu suna zuwa wurin aiki don gwamnati ba zata aminta da rashin zuwa aiki ba sai ranar albashi yace duk wanda aka sama da aikata hakan za a hukunta shi. Nan bada dadewa ba za a rarraba mukaman maikatan kananan hukumomi don bada damar gudanarda mulki yadda ya kamata. Ya godewa shugabanin rikon kwarya kan aikin da suka yi na watanni kafin a rantsar da ciyamom
Ku Tura A Social Media


Share this


Author: verified_user

0 comments: