Kannywood

Dalilan Da Ya Sa Jaruman Arewa Ba Za Su Iya fitowa a Shirin ‘Big Brother’ Ba – Fati SU

A hira na musamman da PREMIUM TIMES tayi da fiattciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Fati SU kan dalilan da yasa jarumai irin su da wasu shahararru a fannin nishadantarwa dake Arewacin Najeriya ba za su iya fitowa a shirin ‘Big Brother’ ba shine ganin yadda sam bai dace da dabi’un mutanen yankin ba da addinin musulunci.

A bayanan da ta yi Fati ta ce tabas za ta so ta sami damar shiga wannan shiri ko dan saboda kyaututtuka da kudaden da ake ci amma sai dai kash hakan bazai yiwu ba saboda ya saba wa kyarwar adininta da al’adun yankin. ” Fitowa a irin wadannan shiri ga mutane irin mu (‘Yan Arewa) ya matukar saba wa adinin mu da al’adanmu a Arewa.
” Misali abubuwan da ‘yan wasan ke yi ya saba wa koyarwar addini na da al’adata kamar sumbatar juna da skey karara, rungumar juna, yadda suke saka kaya suna nuna tsiraicin su baro-baro kuma a nuna a talabijin duniya ta gani. Sannan koda mutum ya yi taurin kai ya shiga cikin shirin, ba karamin suka zai samu ba. Ku duba abin da ya faru da Rahama Sadau, daga jin waka da wani mawakin Jos, Classiq, shikenan sai aka fara sukar ta da ya kai ga har dakatar da ita akayi sannan akayi ta yi mata raddi akai.

Da aka tambayi jarumar game da korafe-korafen da a key cewa jaruman farfajiyar na aikata munanar abubuwa kamar su shaye- shaye da dauran su, Fati ta ce wannan wani abu ne da bata da ansa akai. Fati tace wannan abune da bata san me zata ce a kai ba. ‘‘Ni dai ba abin da zan iya cewa kan wannan tambaya amma kamata ya yi mutane su gane cewa rayuwar dan Kannywood a fim daban yake da rayuwarsa a wajen fim.”

Bayan haka fati ta bayyana yadda wannan shiri na ‘Big Brother Naija’ ya nishadantar da ita inda ta kara da cewa jaruminta shine Tobi da ya zo na uku a shirin. Ta ce sam bata yin Cee C’ da ita ma ta fito a shirin.
A karshe Fati ta ce ta koma makaranta inda take karatun digirin ta na biyu wato PGD. Amma kuma duk da haka bai hana ta fitowa a fina-finai. Sannan kuma ta yabi PREMIUM TIMES sabo d fage da take basu su domin duniya ta san su.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button