Labarai

Babban Shehin yan Shi’a ya Kwance Masu Zani a kasuwa

Rahotanni sun kawo cewa babban Shehin Musulmai mabiya Shi’a, Kamal Al Haidari ya yayewa mabiyansa zani a kasuwa, inda ya bayyana cewa mafi akasarin hadisansu Kirista, Majusawa da Yahudawa ne suka rawaito su.

Shugaban kungiyar na asali, ya furta wannan kalamin a yayin wani shirin talabiji, inda ya ce :

Mafi akasarin hadisan mabiya Shi’a Rafidha, Kirista, Majusawa da Yahudawa suka rawaito su, a ciki har da littafin tafsiri na AL Qomi wanda ya kasance daya daga cikin sanannun litattafai.


“Wadannan litattafan na kunshe da karyace-karyace, kwaskwarima,kazafi da aika-aika marasa misaltuwa, duk da Malam Al Khoei ya nemi tsaftace su.


“Kowa ya san da haka, amma wasu jahilan malamai masu sanye da bakeken alkyabbobi ke ci gaba da rufe ido don yin amfani da su a wajen batar da jama’a”.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button