Sports

Kane Ya Amince Da Sauya Sheka Zuwa Real Madrid

Dan wasan gaba na Kungiyar Tottenham Harry Kane ya
cimma yarjejeniya da Real Madrid kan sauya sheka zuwa
gareta idan aka bude kasuwar ‘yan wasa ta gaba.

Shahararriyar mujallar labaran wasanni ta kasar Spain ‘Don
Balon’ ta rawaito cewa Harry Kane ya amince ya rattabawa
Real Madrid hannu kan yarjejeniyar murza mata leda tsawon
shekaru 5.

Sai dai an cimma matsayar ce tsakanin dan wasan da wakilan
Real Madrid, yayin da a yanzu ya rage, tattaunawa tsakanin
Madrid din da kuma Tottenham kan farashin Harry Kane.

An dai shafe watanni ana alakanta Harry kane da sauya
sheka zuwa Real Madrid tun bayan da tauraruwarsa ta
dada haskawa a fagen zura kwallaye.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button