Labarai

Hukumar Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sakandire (JAMB) Ta Tsayar Da Ranar Yin Jarrabawar Gwaji

Shugaban Hukamar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede

– A sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin jami’inta na hulda da jama’a, Dakta Fabian Benjamin, ta ce za a yi jarrabawar gwajin ranar 26 ga watan nan

– Ana saka ran dalibai 245,753 zasu zauna jarrabawar gwajin daga cikin dalibai 1,652,795 da suka yi rijista da hukumar

Hukumar tsara jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta sanar da ranar 26 ga watan Fabrairu da muke ciki a matsayin ranar da hukumar zata yi jarrabawar gwajin ga daliban da suka yi rijista da hukumar.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya sanar da hakan a yau, Lahadi, a garin Legas.

Benjamin ya ce ana saka ran dalibai 245,753 daga cikin dalibai 1,652,795 da suka yi rijista hukumar ne zasu zauna jarrabawar gwajin.

muna masu farincikin sanar da jama’a cewar hukumar JAMB ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da jarrabawar gwaji ga daliban da suka yi rijista da ita. Mun tsayar da ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2018, a matsayin ranar da za a gudanar da jarrabawar gwajin,” inji Dakta Benjamin.

Dakta Benjamin ya kara da cewar yajin aikin da ma’aikatan jami’o’in kasar nan ke yi ba zai shafi jarrabawar hukumar ba.

Nan bada dadewa ba zamu aika sakon da duk daliban da suka yi rijista da mu zasu yi amfani da shi domin fitar da katin shaidar rubuta jarrabawar,” inji Dakta Benjamin.

Dakta Benjamin ya tabbatar wa da daliban da zasu zauna jarrabawar cewar wannan shekarar ba za a fuskanci wahala wajen rubuta jarrabawar ba kamar yadda aka fuskanta a shekarar da ta gabata ba, domin hukumar ta yi gyare-gyare a kan dukkan da daliban suka fuskanta a bara.

Hukumar JAMB ta ce ta sayar da takardar jarrabawar wannan shekarar ga dalibai 1,966,918 kuma ana saka ran za a gudanar da jarrabawar hukumar a ranar 9 ga watan Maris mai zuwa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button