Kannywood

DUK Da Wahalar Da Nake Sha Banga Ranar Da Zan Daina Acting A Fim Din Hausa Ba -inji Rahama Sadau


Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau, wadda aka dakatar daga shiga harkar Fim, ta bayyana cewa, ta fara shiga matsaloli ne tun bayan da ta fara yin shirin fim din ‘yan kudancin Najeriya da aka fi sani da Nollywood da kuma na turawa wato Hollywood.

Rahama ta bayyana irin yadda take shan bakar wahala daga aftawan Kannywood, tace abu ne marar dadi matuka idan mutun yace zai tsallaka zuwa shirin fina-finan kudancin kasarnan ko na turawa musamman yadda al’adu da dabi’u suka sha bamban.

Ta bayyana cewa, kowadanne masu shirya fina-finai musamman wadan da ake ganin sun saba da dabi’unmu, suna da nasu yanayin gudanarwar harkar fim da ta sha bamban da ta Kannywood.

Rahama Sadau ta yi kira ga ‘yan uwanta masu harkar fim da masu shirin shiga harkar da su sanya damara wajen mai da hankali akan abinda suka sanya a gaba ba tare da wani tsoro ko shakka ba.

“Ina mai baiwa jarumai shawara, da su nutsu su mayar da hankali sosai akan duk abinda suka sanya a gaba, tare da yadda da abinda suke yi, da kuma yadda da zabin da suka yiwa kan, in sun yi haka zasu ci nasara”
“Kasan me kake yi a harkar fim, ka yi aiki tukuru dominsa, tare da jajircewa da kuma tsayawa a kai domin samun nasara da kuma daukaka, in mutum ya maida hankali sosai akan abinda yakeyi to zai ci nasara”


Da aka tambayeta kan rawar da ta taka akan wani sabon shiri mai suna “Zero Hour” Wanda aka kammala aikin daukar shirin a birnin tarayya Abuja, Rahama ‘yar shekaru 24 tace ta fito a shirin fim din a matsayin Zainab ne.

A cikin shirin na fito a matsayin Zainab ne wadda take tsakanin daukar fansar kawunta da aka kashe da kuma batun abokin samartakarta wanda shima yake cikin rudani game da ita a cikin shirin”

Da aka tambayeta kan batun lambar yabo da ta samu daga jaridar Leadership a matsayin jaruma mafi barkwanci ta shekara, tace ta cika da mamakin jin cewar ita ce ta lashe wannan lambar yabo.

@fimhausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button