Labarai

Wani Babban Soja Wanda yayi fice ayaki da Boko Haram Major Hassan (Sarkin Yaki) Ya rasa ransa

Daga Comr Mohammed Pulka

Major Hassan Jajirtaccen Soja ne, kuma haziki wajen yakar Boko haram ajihar Borno Musamman a Yankin Damboa,

Ya hadu da Ajalinsa alokacin da Suke bata kashi da Mayakar Boko Haram a dajin Bita dake kusa da karamar hukumar Damboa na Jihar Borno ranar Jumma’a data gabata.
Mutuwar wannan Namijin Soja ya girgiza Al’ummar Damboa matuka.

Allah ka jikansa sa Rahama, kasa Aljannar Firdausi CE Makomarsa.

Rashin Major Hassan “Babban Rashi ne kuma koma baya ne ga yakin da ake da Boko Haram

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button