Kannywood

Ni Da Fim Mutu Ka Raba, Ko Na Sake Aure Ba Zan Daina Harkar Fim Ba – Khadija Mustapha


Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood watau Khadija Mustapha ta bayyana cewa tana da burin cigaba da harkar fim ko da tayi aure a nan gaba.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da tayi da wata mujallar dake buga labaran masana’antar fina-finan Hausa inda tace tana da burin cigaba da shiryawa tare kuma da daukar nauyin fina-finai koda ta yi aure.

Jarumar ta kuma zayyana yadda ta dade tana sha’awar yin fim tun tana yarinya karama kafin daga bisani ta tsunduma cikin fim din gadan-gadan da kanta.

Tun da farkon tattaunawar dai jarumar ta labarta cewa ita shekarun ta 27 a duniya sannan kuma ta taba yin aure har ma ta haifi ‘ya daya kafin auren nata ya mutu.

Haka zalika jarumar ta bayyana fim din ‘Matar Hamza’ a matsayin wanda yafi kwanta mata a rai saboda yadda ta fita daga Kano zuwa Zamfara domin yin sa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button