Masu Garkuwa Da Mutane Sun Saki Jarumin Fim Al'Amin Buhari Bayan An Biya Diyyar Naira Dubu 500Daga Aliyu Ahmad

Masu garkuwa sun sako jarumin finafinan Hausan nan Al-Amin Buhari bayan an biya Naira dubu 500.

A yayin jin ta bakin Furodusan finanan Hausan nan, Usman Mu'azu ya tabbatarwa da RARIYA  cewa a halin yanzu jarumin yana Abuja, kuma ana sa ran gobe Laraba zai dawo Jos.

Masu garkuwa sun yi garkuwa da jarumin ne a kusa da garin Keffi bayan ya taso daga Abuja zuwa Jos a ranar Lahadin da ta gabata.

Share this


0 comments:

Post a Comment