Labarai

Manyan ‘Yan Kasuwa 20 ‘ Yan Kasa Da Shekaru 40 A Arewa Nigeria Ga Sunayen Kamar Haka

Akwai dalilai da yawa da zaya sanya mutum ya fara kamfani. Amma akwai wani babban dalili mai kyau da ina tunanin kowa ya sanya shi; shine domin a gyara duniya – Phil Libin, CEO din Everton

Wannan jerin sunayen na yan kasuwa yan Arewa an fidda shine daga mutane wadanda sukayi zarra kuma suka taimaka ma mutane. Amfanin wannan ierin sunaye shine ya sanya mutane su san masu kirkire-kirkire daga Arewa wadanda sukayi kokarin kafa kansu da taimada ma yankin Arewa da Najeriya gaba daya. Wannan jerin sunaye kuma zaya taimaka ma wasu masu kirkire-kirkire daga wasu sassan kasar nan domin hada gwiwa da wadanda ke Arewa domin ganin an cigaba. Tawagar Nishadi.tv ta san akwai mutane da dama wadanda sukayi zarra a fannonin tattalin arziki daban-daban, amma jerin sunayen yafi maida hankali ne ga waranda suka tsaya tsayin daka akan hanyoyin kasuwanci. Wanna jerin sunayen na yan kasuwa 20 yan kasa da shekaru 40 ya maida hankali ne akan wadanda suka fara kasuwancin su daga farko har zuwa ya kai ga cin nasara.

Haowa Bello: Madame Coquette
Hauwa wata kwararran mai yin jikkuna ce wanda kuma itace shugabar Madame Coquette, wadanda ke yin jikkuna masu tsada a Najeriya. Ta hanyar yin amfani da mashina kadan, tana hada jikkuna masu kyau daga Leda. Kayan ta ana iya hada su da irin wdadanda ke akwai na zamani a fadin duniya saboda yadda aka hada su. Tayi kokari ta fadada kasuwancin nata zuwa Amurka, Kasashen Turai da fadin Afirika. Duk da sunan datayi, Hauwa na kokari wajen ganin ta inganta hanyar kirkira da hannu da kuma inganta amfani dashi a al’ummar ta. Kayan ta manuni ne akan al’ada da dabi’o’i masu kyau.

Usman Dantata Karami: Anadariya Farms
Ada shi ma’aikacin banki ne kuma mai saya da sayarwa, amma a yanzu yana daga cikin manyan kananan manoma a Najeriya. Anadariya na daya daga cikin manyan masu harkar kayan abinci a kasuwannin Najeriya. Kamfani ne babba mai gonaki, wajen ajiya, kayan sarrafa su, gyarawa, ajiya da kuma izar dasu kasuwa. Yana da burin canza kasar nan da hanyar kasuwanci.

Hadiza A Muhammad: Bilyak Consulting Limited
Ma’aikaciyar banki kuma yar kasuwa, Hadiza tayi aiki a kasar waje kafin ta dawo Najeriya ta fara aiki da Ofishin Microsoft dake Najeriya da Babban Bankin Najeriya. Da Sanin kasuwancin ta, ta dawo kamfanin data taimaka aka assasa, wani babban kamfani mai hudda da kamfanonin layukan waya a Najeriya. Ta taimaka sosai wajen habbaka kasuwancin a kasashewn Afrirka da dama kamar a Kamaru, Afrika ta Kudu, Swaziland, da gida Najeriya. Hadiza itace ta kirkiro wani shafi na kara ilimi na www.mylearningacadem­y.com, wanda yake taimakawa sosai wajen kara karatu. A yan kwanakin baya, ta taimaka da wani tsarin talmaka na yan kasuwa mai suna “Seed funding” domin su tsaya da kafafun su. Wasu daga cikin su sune www.nishadi.tv, wata hanyar nishadantuwa ta yanar gizo, Pree-teens wanda yake akan manhajar IOS da Android, wani shafin bani siga in baka manda na www.arowora.com, wanda babu jimawa za’a fara amfani dashi, da kuma www.yourbusinesshive­.com, hanyar fiddo da masu sana’o’i duniya ta san su. A kwanakin baya ta fiddo da wani tallafi akan shafukan mAcademy da Alfalah domin taimakama dalibi, da kuma wata cibiya domin taimaka ma kananan yan kasuwa su habbaka kasuwancin su.

Zarah Indimi: TulipBistro & Rice Bowl
A matsayin ta na diyar dan kasuwan, Zarah ta koyi abubuwan kasuwanci daga gare shi inda ta fara nata daga farko izuwa nasarar data samu a yanzu. A matsayin ta na yar kasuwa, wajen cin abincin ta na daya daga cikin wurare mafi kyawu da mutum zaya ci abinci a Abuja. Suna da jama’a sosai kuma suna da dahuwa ta gida Najeriya da kasashen waje. Ta fadada Tulip Bistro zuwa wurare daban-daban inda ta fadada kasuwancin kuma ta samar da damarmaki ga mutane da yawa. 

Railwan Hassan: Focal point Cleaners
Hassan yana da sama da shekaru 16 na kasuwanci, aiki a gidan jarida, da kuma Noma. Wannan mutum ne wanda yake da hangen nesa kuma yake tafiya tare dashi. Ya kasance cikin wani kwamiti wanda ya taimaka wajen fiddo da hanyar karatu ta Madrasah wadda ake amfani da ita a Arewacin Najeriya. Hassan yana taimaka ma ilimi ta hanyar kungiyar sa kanshi ta “Sardauna Child Foundation”, wadda take taimaka ma marayu domin dauke su daga kan tituna ta kai su makarantu. A yanzu shine Manajan Focal Point Group, wanda keda ra’ayi a gine-gine, Noma, Publishing da gurza takardu, lallai shi yana canza hanyar kasuwanci ta duniya.

MANYAN YAN KASUWA 20 YAN KASA DA SHAKARA 40 bincike da nishadi.tv ta a’iwatar

Akwai dalilai da yawa da zaya sanya mutum ya fara kamfani. Amma akwai wani babban dalili mai kyau da ina tunanin kowa ya sanya shi; shine domin a gyara duniya – Phil Libin, CEO din Everton

Wannan jerin sunayen na yan kasuwa yan Arewa an fidda shine daga mutane wadanda sukayi zarra kuma suka taimaka ma mutane. Amfanin wannan ierin sunaye shine ya sanya mutane su san masu kirkire-kirkire daga Arewa wadanda sukayi kokarin kafa kansu da taimada ma yankin Arewa da Najeriya gaba daya. Wannan jerin sunaye kuma zaya taimaka ma wasu masu kirkire-kirkire daga wasu sassan kasar nan domin hada gwiwa da wadanda ke Arewa domin ganin an cigaba. Tawagar Nishadi.tv ta san akwai mutane da dama wadanda sukayi zarra a fannonin tattalin arziki daban-daban, amma jerin sunayen yafi maida hankali ne ga waranda suka tsaya tsayin daka akan hanyoyin kasuwanci. Wanna jerin sunayen na yan kasuwa 20 yan kasa da shekaru 40 ya maida hankali ne akan wadanda suka fara kasuwancin su daga farko har zuwa ya kai ga cin nasara.

Haowa Bello: Madame Coquette
Hauwa wata kwararran mai yin jikkuna ce wanda kuma itace shugabar Madame Coquette, wadanda ke
yin jikkuna masu tsada a Najeriya. Ta hanyar yin amfani da mashina kadan, tana hada jikkuna masu kyau daga Leda. Kayan ta ana iya hada su da irin wdadanda ke akwai na zamani a fadin duniya saboda yadda aka hada su. Tayi kokari ta fadada kasuwancin nata zuwa Amurka, Kasashen Turai da fadin Afirika. Duk da sunan datayi, Hauwa na kokari wajen ganin ta inganta hanyar kirkira da hannu da kuma inganta amfani dashi a al’ummar ta. Kayan ta manuni ne akan al’ada da dabi’o’i masu kyau.

Usman Dantata Karami: Anadariya Farms
Ada shi ma’aikacin banki ne kuma mai saya da sayarwa, amma a yanzu yana daga cikin manyan kananan manoma a Najeriya. Anadariya na daya daga cikin manyan masu harkar kayan abinci a kasuwannin Najeriya. Kamfani ne babba mai gonaki, wajen ajiya, kayan sarrafa su, gyarawa, ajiya da kuma izar dasu kasuwa. Yana da burin canza kasar nan da hanyar kasuwanci.

Hadiza A Muhammad: Bilyak Consulting Limited
Ma’aikaciyar banki kuma yar kasuwa, Hadiza tayi aiki a kasar waje kafin ta dawo Najeriya ta fara aiki da Ofishin Microsoft dake Najeriya da Babban Bankin Najeriya. Da Sanin kasuwancin ta, ta dawo kamfanin data taimaka aka assasa, wani babban kamfani mai hudda da kamfanonin layukan waya a Najeriya. Ta taimaka sosai wajen habbaka kasuwancin a kasashewn Afrirka da dama kamar a Kamaru, Afrika ta Kudu, Swaziland, da gida Najeriya. Hadiza itace ta kirkiro wani shafi na kara ilimi na www.mylearningacadem­y.com, wanda yake taimakawa sosai wajen kara karatu. A yan kwanakin baya, ta taimaka da wani tsarin talmaka na yan kasuwa mai suna “Seed funding” domin su tsaya da kafafun su. Wasu daga cikin su sune www.nishadi.tv, wata hanyar nishadantuwa ta yanar gizo, Pree-teens wanda yake akan manhajar IOS da Android, wani shafin bani siga in baka manda na www.arowora.com, wanda babu jimawa za’a fara amfani dashi, da kuma www.yourbusinesshive­.com, hanyar fiddo da masu sana’o’i duniya ta san su. A kwanakin baya ta fiddo da wani tallafi akan shafukan mAcademy da Alfalah domin taimakama dalibi, da kuma wata cibiya domin taimaka ma kananan yan kasuwa su habbaka kasuwancin su.

Zarah Indimi: TulipBistro & Rice Bowl
A matsayin ta na diyar dan kasuwan, Zarah ta koyi abubuwan kasuwanci daga gare shi inda ta fara nata daga farko izuwa nasarar data samu a yanzu. A matsayin ta na yar kasuwa, wajen cin abincin ta na daya daga cikin wurare mafi kyawu da mutum zaya ci abinci a Abuja. Suna da jama’a sosai kuma suna da dahuwa ta gida Najeriya da kasashen waje. Ta fadada Tulip Bistro zuwa wurare daban-daban inda ta fadada kasuwancin kuma ta samar da damarmaki ga mutane da yawa. 

Railwan Hassan: Focal point Cleaners
Hassan yana da sama da shekaru 16 na kasuwanci, aiki a gidan jarida, da kuma Noma. Wannan mutum ne wanda yake da hangen nesa kuma yake tafiya tare dashi. Ya kasance cikin wani kwamiti wanda ya taimaka wajen fiddo da hanyar karatu ta Madrasah wadda ake amfani da ita a Arewacin Najeriya. Hassan yana taimaka ma ilimi ta hanyar kungiyar sa kanshi ta “Sardauna Child Foundation”, wadda take taimaka ma marayu domin dauke su daga kan tituna ta kai su makarantu. A yanzu shine Manajan Focal Point Group, wanda keda ra’ayi a gine-gine, Noma, Publishing da gurza takardu, lallai shi yana canza hanyar kasuwanci ta duniya

Abdulrahman Aliyu: Zavati Group
Kasuwanci na bukatar hangen nesa, zuciyar yi, da naci, Abdulrahman lallai yana dasu duka. Dan kasuwa mai kungiyoyin kamfanoni na Zavati wanda suka fi maida hankali a gine-gine, harkar kudade da saka hannun jari. Dan kasuwa ne wanda yake da hannaun jari, yana taimakawa sosai musamman ga kananan yan kasuwa ta hanyar shugabancin shi.

Laura Ahman: Laura Ahman brand
Laura Ahman wata mai takalma ce mai tasowa wadda ta fara aikin takalma a Watan Fabraairu na 2014. Daya daga cikin manyan masu takalma a Arewacin Najeriya da Najeriya gaba daya, Laura Ahman ta fara babu jimawa amma ta samu nasarori inda ta nuna ma jama’a ammfanin mutum ya jajirce akan abunda yasa gaba. Irin takalman da take yi ya sanya ta ta zama wadda ake so a fadin Najeriya. Duka takalman nata da hannu ake yin su ta hanyar Leda daga Arewacin Najeriya.

Nasir Abdulkadir Yammama: Verdent Agri-Tech
Banda zama dan kasuwa mai rajin kasuwanci, shi mai kirkirar kayan na’ura mai kwakwalwa ne. Ya kasance daga cikin wanda suka samu koyarwar kasuwanci daga Sir Richard Branson a 2014, wanda ya kara mashi sanin kasuwanci. Kasancewar Nasir a kasuwanci ta fara ne daga kamfanin shi Verdant Agri-Tech, wanda ke taimaka ma Manoma domin inganta hanyoyin kasuwancin su. Ba wai kawai yana taimakawa wajen harkar Noma bane, yana taimaka ma matasa da dama wurin nuna masu kasuwanci da Na’ura mai kwakwalwa.

Laylah Ali Othman: L and N Interiors
Laylah itace shugabar kamfanin gyaran cikin gidaje na L and N Interiors dake a Abuja. Laylah Othman ba wai kawai tana nuna bajintar ba a sana’ar ta, tana kuma magantawa akan abubuwan da suke shafar mata a cikin al’umma. Ta fadada kasuwancin ta inda ta taimaka ma mutane da yawa, kuma ayanzu ta shiga harkar Mujalla wanda ta fara babu jimawa.

Huda Fadoul Abacha: Hudayya
Huda Fadoul itace shugabar kamfanin kayan sawa da kayan Amare dake a Najeriya. Tana dinka kaya masu tsada na Amare. A matsayin ta na yar kasuwa, Huda bata boye ilimin ta na dinki ba, ta gina wata makarantar koyon kayan kyalkyali da dinki domin inganta rayuwar su. Kwarewar ta na fitowa a cikin kayayyakin ta da mutane ka iya gani a zahiri.

Fantis Mohammed; H Magnet
Fantis Mohammad asalinta yar Borno ce, wanda aka hada H Magnet da ita, shugabar Santi Food da kuma kamfanin dinki na Nowrie. Kamfanin Santi na a Abuja ne kuma tana da burin zama mafi girma a Arewacin Najeriya. A matsayin ta na mai kayan sawa, kayan ta nada mutunci ga ya’ya mata. Fantis nada ra’ayi a game da kasuwanci da taimaka ma mata da basu shawarwari. 

Labila kabir: Asoebicouture
A duniyar kyalekyale inda kayan mata ke a sama, Labila Kabir ta kai kololuwa wajen sarrafa yaduka da kayan sawa. Ba tare da wani masaniya ba akan kasuwanci, sai dai burin samun nasara, Labila tayi nasarar cimma burin ta, wanda hakan ya haifar da Asoebi Couture. Yadda take sarrafa kaya yayi tasiri sosai a Arewacin Najeriya a yau. Wannan ya sanya ta ta zama ta farko wadda ake zuwan wajen ta domin kaya masu kyau.

Hyaledzira Laushi: Blueeyelvetmarquee
Kusan itace ta farko wajen kawo sana’ar shirya bukukuwa da tsara su a Abuja. Tana daya daga cikin masu tunanin gaba a cikin masana’antar a yau. Da irin ilimin dake gare ta, tana shirya azuzuwa ga masu hada bukuwa daga ko ina daga fadin Afirika. Lokaci da dama ta nuna cewa tana iya hada irin bikin da mutum yake so, ta yadda yake son shi.

Khalifa Dankadai; Khalifa Dankadai & Company
Mai taikama ma al’umma, dan kasuwa, yana taimaka ma matasa da matan Afirika domin citaban su. Khalifa yayi imani cewa kowa, musamman Almajirai ya kamata su samu ilimi da hanyar sana’a domin cigaban al’umma. Shi dan kasuwa ne wanda ya taimaka ma mata da matasa a Arewacin Najeriya.

Fatima Mamza: Mamza Beauty Limited
Kamfanin Mamza na kwalliya ne da gyaran jiki wanda ke a Abuja, Najeriya. Kwarewar Mamza musamman wajen sanya mutane suyi kyau da sanya su jin cewa sunyi kyau ya sanya ta zama ta gaba wadda ake zuwa wurin ta a Najeriya. Banda kwalliya data ke yi, tana bada shawarwari akan gyaran jiki, kwalliya da kuma kulawa da jakin. Ta samu kwarin gwiwa daga daukar hotuna, kwalliya, tarihi, da al’ada. Mamza na kokari wajen ganin cewa ta yi fice kuma ta zama ta gaba a harkar kwalliya.

Samira Garba Abari: Patooty Nigeria Enterprises
Shugabar kamfanin Patooty ta canza hanyar kwalliya a Arewacin Najeriya da yadda ake hada man kwakwa da Shea butter. Tana da shafin dake basu damu suna cinma kastomomin su a kai tsaye a ko ina a fadin duniya. Tayi kokari sosai ta kafa kanta inda ta zama abun ambato a gidaje a Najeriya inda manyan kamfanoni ke neman ta.

Muhammad Ibrahim Jega: Startup Arewa
A matsayin shi na mai kirkire-kirkire, dan gwagwarmaya, kuma manaja mai alkakkin cigaban kasuwanci a Vogue pay, kuma wanda ya kirkiri Startup Arewa, Muhammad Mutum ne wanda yake so ya daga kasuwanci a Arewacin Najeriya. Ta hanyar kasuwancin shi, yayi kokari sosai domin taimaka ma matasa su kama sana’o’i daban-daban.

Mukhtar Ibrahim Aliyu: Urban Abode Nigeria Limited
Wannan matashin ya kwashe shekaru da dama inda ya daga kamfanin shi na “Urban Abode” daga farko zuwa nasarar da yaci a yanzu. Neman ginannen gida mai kyau ba karamin abu bane amma Urban Abode ya nuna cewa na daban yake. A matsayin shi na mai zana gidaje, ya fito da kanshi a matsayi gogagge a Arewacin Najeria.

Mario Abdullah: kamu Decor
Tambayi wani game da Kamu decor zasu gaya maka Mairo Abdullahi. Tayi kokari sosai wajen sake fiddo da kamu ta hanyar zamani daga yadda yake ada. Kokarin ta wajen inganta aiyukan ta ya sanya tayi zarra sosai a Arewacin Najeriya. kokarin ta ya kawo sauyí sosai a kasuwar bukuwa a Najeriya.

Fatima Oyizah Ademoh: Ajima Youth
Lakchara, Monomiya, yar kasuwa, kuma mai taimakawa wajen gogagad da matasa akan kasuwanci. Ita keda wata hanyar samar da wautar lantarki a kauyuka mai suna Ajima farms off-grid energy. Tana daga cikin masu taimakawa domin gaggadda matasa ta hanyar kasuwanci mai suna TEEP da shahararren dan kasuwa mai suna Tony Elumule ya assasa. Tayi nasarar taimakama kauyuka da dama wajen samar masu da haske domin inganta rayuwar mutanen karkara.
————————–

Gidan Talbijin Nishadi ne ya gudanar da wannan binciken don zaburar da matasa kan muhimmanci sana’a

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button