Kannywood

Kannywood :-Lokacin Da Na Fara Fim Sai Da Gaba Na Ya Fadi, Cewar Bilkisu Abdullahi



A ko da wanne lokaci idan ka leka masana’antar finafinai ta Kannywood sai ka ga sababbin fuskoki maza da mata su na shigowa domin su ma su gwada tasu basirar. Bilkisu Abdullahi ta na daga cikin irin wadannan jaruman. Ta shigo harkar ne a ’yan watannin nan. Wakilin mu, MUKHTAR YAKUBU, ya nemi ji ta bakin ta a game da dalilin shigowar ta harkar fim da kuma barin da ta ke da shi.

FIM: Da farko dai za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.
BILKISU ABDULLAHI: To, assalamu alaikum. Ni dai suna na Bilkisu Abdullahi, kuma ni a garin Legas aka haife ni a shekarar 1993. Can na yi karatu na na firamare da sakandire, kuma daga baya na dawo Kano.

FIM: Harkar fim ce ta dawo da ke Kano?
BILKISU: A’a, ba harkar fim ce ta dawo da ni ba. Ni mahaifi na dan Kano ne, to kuma Allah Ya yi masa rasuwa, mahaifiya ta na auren wani mijin daban, don haka sai na dawo wajen dangin uba na da zama.

FIM: Ita mahaifiyar ki ’yar ina ce?

BILKISU: To ita mahaifiya ta Bafulatanar Yola ce ta Jihar Adamawa, amma dai yanzu ta na zaman aure a Legas. Tun baban mu ya na raye a can ta ke. To da ya rasu ma a can ta kara yin aure.
FIM: To yaya aka yi ki ka samu kan ki a harkar fim? Da man ki na sha’awa ko sai da ki ka zo Kano?

BILKISU: E, gaskiya da man ina sha’awa, don ina kallon finafinan Hausa tun ban kai ga haka ba kuma ina sha’awar abin, ya na burge ni sosai. Sai dai a lokacin ina ganin ba zan iya ba saboda ban san yadda zan hadu da masu yi ba, kuma ga shi ina karama.
FIM: Ta yaya aka yi ki ka samu kan ki a harkar fim?

BILKISU: E, to ni dai ba zan iya cewa ga lokacin ba sai dai na ce a cikin ’yan watannin nan na shigo, don ban dade da shigowa ba. Kuma dan’uwa na ne ya kawo ni ya gabatar da ni, daga nan aka kawo ni wajen Baba {arami kuma a lokacin ya fara sa ni a cikin fim din sa mai suna ‘[akin Duhu’, kuma shi ne fim din da na fara yi. Amma dai a yanzu an fara kira na ana sanar da ni finafinan za a yi kuma zan fito a ciki.
FIM: Wanne matsayi ki ka taka a fim din?
BILKISU: Na fito ne a matsayin kanwar jarumar fim din, sai mu ka hadu da wani saurayi a cikin A-daidaita-sahu, ya ce na ba shi lamba ta, na ce ai na fi karfin ajin sa, daga baya sai na gano mai kudi ne, sai kuma na zo ina yin da-na-sani.

FIM: Ba ki samu matsala a gida ba da ki ka shiga harkar fim?

BILKISU: Gaskiya babu wata matsala da na samu, don ita mahaifiya ta ma ta na son fim. 
Kuma duk wani abu da ake fada ma a kan ’yan fim ni da na zo ban gani ba.

FIM: Kafin ki shigo harkar fim ki na jin labarin ’yan fim ne, kuma ko da kin gan su ma sai dai gani daga nesa. Yanzu da ki ka hadu da su ki ka gan su, yaya ki ka ji?

BILKISU: Gaskiya na ji dadi sosai. Da, ina ganin abin ma kamar a mafarki, na ga Ali Nuhu da Adam A. Zango duk mun yi magana da su; amma yadda ake ta bada labarin su na da girman kai ni ban gani ba. Mun yi magana da su sosai.

FIM: Ke sabuwar jaruma ce. Da a baya zama ki ke yi kawai ki na kallon fim a yanzu da ki ka fara yaya ki ka ji yadda harkar ta ke?
BILKISU: To, (dariya) gaskiya ’yan fim su na kokari domin ban san haka abin ya ke ba sai da na zo na fara sai na ji ashe wahala ake sha sosai. Don lokacin da na fara sai da gaba na ya fadi, na ji kamar ba zan iya ba, amma dai da na daure na sa wa zuciya ta zan iya sai na ci gaba.

FIM: Amma dai a yanzu kin yi gogewar da za ki iya fitowa a kowanne fim?
BILKISU: E to, ka san abin sai a hankali amma dai na san zan kokarta. Sai nan gaba zan iya wannan bugun kirjin. Ka san ni bakuwa ce.

FIM: Wanne irin buri ki ke da shi a game da harkar fim?
BILKISU: Ni dai buri na shi ne na zama babbar jaruma yadda duniya za ta san ni. Kuma ina fatan Allah Ya sa na gama da harkar fim lafiya.

FIM: Daga karshe ko ki na da wani sako?
BILKISU: Sakon da na ke da shi shi ne godiya ce ga ubangida na, Abdullahi Sani Abdullahi (Baba Karami) domin shi ne ya fara saka ni a fim kuma a yanzu a kamfanin sa na ke
.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button