Kannywood: Bazan Auri Dan Fim Ba Kowanene – Nafisa Abdullahi

Fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ba zata auri ɗan Fim ba kowanene, kasancewar tana da samari da yawa kuma a halin yanzu ta fitar da wanda zata aura.

Jarumar dai tayi wannan jawabi ne ga wata majiya, inda aka tambaye ta shin ko mene dalilin da yasa ake sa ranar bikinta amma kuma ake fasawa? Sai ta amsa da cewar ita dai a iya saninta ba ta san da wannan magana ba, wata kila masu wannan maganar sune suke sa mata ranar bikin nata.

Ta ci gaba da cewa ita dai abinda ta sani shi ne tana da masoya da dama kuma ita tun tuni ta fitar da wanda ta ke so kuma shi za ta aura cikin izinin Allah anan gaba kaɗan kuma shi ba ɗan fim bane.

Share this


0 comments:

Post a Comment