Saudiyya Ta Kai Wa Musulman Myanmar Dauki (Burma)
A yayin da al'ummar Musulmin Rohingyar a kasar Myanmar ke fuskantar ukuba daga arna, kasar Saudiyya bisa jagoranci Sarki Salman, ta bayyana ba su tallafin Dala Miliyan Hamsin.

Haka kuma, baya ga tallafin wadannan kudi masu tsoka, ta amince da ba adadin Musulmin na Rohingyar guda Miliyan Daya mafaka a Saudiyya.

Wannan shi ne babban tallafi na farko da ya fito daga wata kasar Musulunci.

Allah Ya taimaka wa Musulmin Myanmar, Ya cece su daga wannan bala'i da suke fuskanta. Amin!

Share this


0 comments:

Post a Comment