Jiragen ruwa 26 dauke da man fetur da kayayyakin abincin zasu iso jihar Lagas


Jiragen ruwa guda ashirin da shida ne ake tsammanin saukar su a tashar jirgin ruwa dakeApapa da Tin-Can Island dake Lagas daga ranar 7 zuwa 23 ga watan Satumba, jiragen zasu zo dauke da man fetur, kayan abinci da sauran kaya.

Hukumar tashar jirgin ruwa (NPA) ta bayyana haka ne ga rubuce rubucenta, ‘Shipping Position’, hukumar ta bayyana haka ne gakanfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a Lagas.

Hukumar tashar jirgin ruwa tace jiragen suna dauke da alkama, masara, suga, man-gyada, kwantena, kifaye, gishiri, fetur da kwantena dauke da kayayyaki.


Jiragen ruwa 26 dauke da man fetur da kayayyakin abincin zasu iso jihar Lagas
Kanfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa jirage 10 sun sauka a tashar jirgin ruwa dauke da taki, masara, kayan karafuna, man diesel da fetur.


Kamfanin ta kuma rahoto cewa wasu jirage 22 a halin yanzu suna tashar jirgin ruwa inda ake sauke alkama, masara, taki, suga, kifi, man fetur man ja da sauran kayan masu amfani.

Sources:naijhausa.com

Share this


0 comments:

Post a Comment