EFCC Ta Sake Kama Jami'anta Da Ke Fasa Gidajen Da Hukumar Ta KwaceHukumar EFCC ta kama daya daga cikin direbobinta wanda ya kware wajen fasa gidajen da hukumar ta kwace daga hannun barayi inda aka samu nasarar kama shi a lokacin da yake kokari fasa gidan Tsohon Shugaban Hafsoshin Sojan Nijeriya, Alex Badeh da ke Abuja.

Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwajaren ya ce an kama direban mai suna Nasiru Isa ne da wani dan sanda mai suna Ismaila Aliyu da kuma wasu abokan aikinsa da ya bayyana sunayensu kamar haka ;Abubakar Jibrin, Abdulsalam Ado, Ibrahim Babangida, Reuben Dauda, Hassan Aliyu, Sani Yusuf  da Murtala Mohammed.

Sorces:Rariya

Share this


0 comments:

Post a Comment