Uncategorized

BREAKING :Trump da Clinton na kan-kan-kan a muhimman jihohi

Donald Trump da Hillary Clinton na tafiya kan-kan-kan a muhimman jihohi da fafatawa ta yi zafi sosai.
Babu tabbas kan inda sakamakon zai kaya a jihohin da suka hada da Florida da kuma Virginia.
Tuni Mista Trump ya lashe kujerun jihar Ohio da gagarumin rinjaye.
Gidan talabijin na ABC News ya yi hasashen cewa Mista Trump ya yi nasara a jihohin Kudancin kasar, yayin da Hillary Clinton ta samu galaba a jihohin Arewa.
Har ila yau ana sa ran jam’iyyar Republican za ta rike rinjayen da ta ke da shi a majalisar wakilan kasar.
Ana bukatar dan takara ya samu kuri’u 270 daga cikin manyan kuri’u 538 (wato electoral college) domin samun nasara.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta BBC ta nuna cewa Clinton na gaban Trump da maki hudu kacal.
Da sanyin safiya misalin karfe 06:00 ne aka fara kada kuri’a a Gabashin kasar, sai dai tuni wasu kauyuka a jihar New Hampshire sun riga sun kada kuri’unsu.
Duka Misis Clinton da Mista Trump sun kada kuri’unsu a mazabu daban-daban a birnin New York.
An samu dogayen layuka a wasu jihohin, abin da ke nuna yadda jama’a suka fito sosai.
Wasu wuraren kada kuri’ar sun samu matsalolin na’ura, abin da ya haifar da jinkiri.
Duka ‘yan takarar sun yi gangamin yakin neman zabe a jihohin North Carolina da Pennsylvania da kuma Michigan, inda nan ne takarar ta fi zafi.
Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa kuri’unsu a jihohin da suka bude rumfunan zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta zaben gama-gari.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan asalin Latin Amurka masu amfani da yaren Spaniya, wadanda ke goyon bayan Hillary Clinto, sun fito sosai.
Hillary Clinton da Donald Trump sun zagaye kasar domin neman kuri’un jama’a a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button