FATAWAR RABON GADO (58)|Dr.jamilu yusuf zarewa

FATAWAR RABON GADO (58)
Tambaya:
Assalamu Alaikum. mal Allah saka da gidan Aljannah. malam inatambaya mahaifiyata ce Allah ya amshi rayuwarta ta bar mahaifiyarta da maigidanta da ni  namiji 1 sai mata su 6. ya gadon zai kasanche. Allah yakara wa Malam lafiya amin
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida:12, Sai a bawa mijinta kashi:3, mahaifiyarta kashi:2, ragowar sai a bawa 'ya'yanta su raba duk namiji ya dau rabon Mata biyu.      
Aĺlah ne mafi sani
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.

Share this


0 comments:

Post a Comment