YA AKE ZAMA GWANI A HARKAR KWAMFUTA?

               Daliban koyon karantun kwamfuta

Babu yadda za ayi dalibi ya kware a harkar kwamfuta matukar bai mayar da hankalinsa wurin abin da malamansa suke koya masa ba.
Wani lokaci ba matsalar dalibai ba ce, matsalar abin da zasu yi practice da shi shi ne matsala. Wadansu kuma a lokacin da suke koyan karatun hankalinsu baya wurin malamin.

Idan mutum yana son ya kware kuma ya zama gwani a duk harkar da ya sa a gabansa to ya sani sai ya baiwa wannan abun mahimmanci.
Misali zaka samu dalibai kowa na kokarin ya mallaki kwamfuta amma kuma da zarar ya samu ba shi da abin da zai yi da ita face kallon fina-finai ko kuma yin game ko kuma sauraron wakoki.
Ya ake zama gwani a harkar Kwamfuta? Hanya daya ce, ka daukarwa kanka cewar ina son in zama kwararre a wannan fanni ta hanyar yin kokarin ganin kana aikata ayyukan da aka umarce da su a makaranta.
Wani abu da yake kara goge dalibai shi ne lokacin da dalibi ya dauki ragamar kara fadada bincike da maimaita ayyuka da malamai ba su saka shi ba.
Misali ba yadda za ayi a ce ka san me zaka yi, kawai ka dauko kwamfuta ka bude MS Word, ko Excel, ko Access, ko CorelDraw da makamantansu baka san mene ne dalilin da ya sa na bude su ba.
Misali idan kana koyan aikin Graphics da CorelDraw (Duk da cewar ba a yi shi don Graphics ba) to idan kana son ka zama gwani sai ya kasance kana daukan wadansu takardu da aka yi Graphics din a ciki kana kwatantawa.
Yin haka lallai zai taimaka maka wajen gano mene ne na iya mene ne ban iya ba, a wannan lokaci zaka ga ka kara kwarewa a wani bangare da da iya shi kayi, za kuma ka ga ka fahinci wani abu da da baka ma gane me ake nufi da shi.
Wassalam
Posted  by sadeeqmedia boss
Fb:Abubakar Rabiu Yari
Whatsapp/call:09032038203

Share this


0 comments:

Post a Comment